Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Eden Hazard Ya Ce Zai Koma Real Madrid Saboda Zinedine Zidane


Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Genoa dake kasar Itali sun Kalli wasa na minti 43 na farko lokaci a wasansu na gida da suka yi da Empoli a gasar Seria A mako na biyu cikin shiru, a matsayin jimami ga mutane 43 da suka rasa rayukansu a lokacin da wata gada ta rushe a cikin kasar ta Italiya a farkon watan Agusta.

Tun kafinn fara wasan sai da kungiyoyin biyu suka yi shiru na minti guda (silence) saboda da nuna alhininsu game da mutuwar mutanen, an dai tashi a wasan kungiyar Geanoe ta doke Empoli da ci 2-1, dan kwallon Everton Theo Walcott, wanda bai samu shiga cikin tawagar Ingila ba har tsawon shekaru biyu, ya ce zai koma cikin tawagar kungiyar ta Ingila nan gaba.

Dan wasan Baya na Tottenham Danny Rose, mai shekaru 28, na shirin komawa kungiyar kwallon kafa ta Marseille, a matsayin aro ko kuma dindindin domin ya samu kansa a tawagar kasar Ingila.

Manchester United, ta ce bata nemi dan wasan baya na Tottenham Danny Rose, da kuma Toby Alderweireld, a wannan kakar wasannin ba sakamakon alakanta ta da ake yi da neman ‘yan wasan.

Kocin Newcastle, Rafael Benitez, ya ce yana jin daɗin jinkirta tattaunawa game da makomarsa a kungiyar har zuwa shekara ta gaba wadda aka sa ran zai sabunta kwangilar kafin kakar wasan, ya ce yana "tunani ne kawai game da wasanni".

Dan wasan Chelsea Dan kasar Belguim Eden Hazard, mai shekaru 27, ya ce dama zai bar Chelsea ya koma Real Madrid ne saboda Zinedine Zidane na matsayin kocin kungiyar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG