Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duniyar Fina Finai Tare Da Jaruma Sadiya Adamu


Sabuwar Jaruma Sadiya Adamu
Sabuwar Jaruma Sadiya Adamu

A shirin mu na wannan makon mun samu zantawa da sabuwar Jaruma Sadiya Adamu, wacce ta fara harkar fim shekaru biyu da suka wuce, wadda tace ita dai burinta shine ta fadakar da al’umma kafin ta samu mijin aure.

Cikin tattaunawar su da wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir, ta bayyana mata sha’awa fim ce ta ja hankalin ta ga wannan harkar, kasancewar tun tana karama take kallo wasannin Hausa fim ta haka ne ta fara sha’awar ita ma ta zama jaruma, daga baya kuma ta fahimci sana’a ce mai kawo kudi.

Fim din da tafi tashe sune “Siyan Baki” da “Kibiyar Ajali” da “Matar Baki.” Tunda daga makarantar sakandare bata ci gaba da karatu ba amma tana da burin komawa ta karo ilimi.

Sadiya dai tana da burin Allah ya kawo mata miji tayi Aure, tace idan har mijin aure yazo zata bar harkar fim. Kuma bata fuskantar wani kalubale a yanzu haka domin tana zaune da kowa lafiya, tana kuma addu’ar ita ma Allah ya kaita kamar inda yakai sauran Jarumai a wannan harka ta fina finai.

XS
SM
MD
LG