Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Wasan Super Eagles Ya Fara Samun Sauki Na Komawa Gasar AFCON


Samuel Kalu

Likitoci sun bada tabbacin cewa dan wasan tawagar kwallon kafa ta Super Eagle's ta Najeriya Samuel Kalu, ya fara samun sauki kuma zai iya tallafa wa Najeriya a gasar da ake bugawa na cin kofin kasashen Afrika na 2019 wacce kasar Masar ta dauke nauyi.

Kalu dai ya fadi ne a lokacin da tawagar 'yan wasan suke karban horo tun kafin wasan su na farko a gasar kasashen Afrika, wanda suka samu nasara akan kasar Burundi daci 1-0 inda nan take aka garzaya da shi asibiti domin sani abunda yake faruwa da shi.

Inda likitoci suka tabbatar da cewar zuciyar dan wasan ce ta buga a lokacin da suke karban horon, sai dai kuma a halin da ake ciki sun ce sun shawo kan matsalar kuma dan wasan zai fara atisaye nan da wasu kwanaki tare da 'yan wasa.

Hakan yasa mai horas da tawagar ‘yan wasan na Super Eagles ta Najeriya, Gernot Rohr, yace ya samu kwarin gwiwa ganin cewar dan wasan ya fara samun sauki sosai kuma zai iya taimaka wa Najeriya a gasar.

Najeriya dai tana mataki na daya ne a rukunin (B) da maki 6 bayan da ta doke kasar Guinea daci 1-0 a wasa na biyu cikin rukunin, hakan ya bata damar samun tikitin zuwa zagayen wasan kasashe 16, a ranar Lahadi 30 ga watan Yuni zata fafata da Madagasca a wasa na uku cikin rukunin.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG