Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Wasan Kungiyar Kwallon Kafar Arsenal Zai Dawo A Sabuwar Shekara


Jack Wilshere
Jack Wilshere

Dan wasa Jack Wilshere na kungiyar kwallon kafar Arsenal zai dawo a sabuwar shekara.

Kungiyar kwallon kafar Arsenal ta karyata batun da ake yi cewa dan wasan ta na tsakiya Jack Wilshere ya fuskanci damuwa bayan daya dawo daga jinyar rashin lafia idon kafarshi.

Shi dai ba Ingilen dan wasan kasa-da-kasar ya samu mumunar rauni a jijiyarshi a wasan da suka buga wanda suka ba kungiyar kwallon kafar Manchester United kashi da ci 2-1 a watan Nuwamba, wanda da ga baya ya tafi jinya na watanni uku.

A wani rahoto da jaridar Ingila ta fitar ranar Litinin, an shiryar da tura dan wasan Wilshere hutu na tsawon watannin 5 a dalilin dadewar da yayi yana jinya don ya samu isashiyar lafia.

Amma daraktan sadarwa na kungiyar Mr. Mark Gonnella ya musanta wannan maganar, ya tabbatar da cewar dan wasa Wilshere ya na wani Kos wanda zai dawo a sabuwar shekara.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:51 0:00
Direct link

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG