Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Wasan Kungiyar Inter Milan Ya Bukaci Komawa Arsenal


Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan, Ivan Perisic, ya bayyana burinsa kan komawa kulob din Arsenal bayan da Inter Milan ta ce a shirye take data sayar dashi.

Dan wasan Perisic yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka taimakawa kasar Crotia ta kai ga wasan karshe na gasar cin kofin duniya da aka buga a kasar Rasha a 2019, ya bayyana kudirinsa na barin kungiyar tun a baya, amma hakan bai yuwu ba.

Kungiyar Arsenal dai tana daya daga cikin kungiyoyin da suke sha'awar ganin sun dauko dan wasan, kuma tuni ta fara shirin fara magana da Inter Milan akan sayensa.

Sai dai mai horas da Arsenal, Unai Emery bashi da kudaden da zai iya sayan ‘yan wasa da yawa, sakamakon kungiyar ta ware fam miliyan £45 kacal domin sayan sababbin ‘yan wasa a kakar wasan bana a yanzu haka.

A kakar wasan da ta gabata Ivan ya jefa kwallaye 9 cikin wasanni 45 daya buga wa Inter Milan.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG