Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Chelsea Ta Sa Eden Hazard A Matsayin Na Farko


Kungiyar kwallon Kafa ta Real Madrid ta sanya dan wasan gaba na Chelsea Eden Hazard, a matsayin shine na gaba gaba cikin jerin ‘yan wasan da take nema Domin maye gurbin Cristiano Ronaldo, wanda ya koma Juventus da taka leda inda ake sa tsammanin mai tsaron raga na kungiyar Chelsea, Thibaut Courtois, mai shekaru 26 zai koma Kungiyar ta Real Madrid akan kudi fam miliyan 31.

Idan har Chelsea ta sayar da Courtious da yuwuwar zata dawo da tsohon golanta Petr Cech dan shekaru 36 daga Arsenal, ko kuma mai tsaron raga na Leicester City Kasper mai shekaru 31 da haihuwa.

Dan wasan Gaba na Westham Marko Arnautovic mai shekaru 29 a duniya na shirin komawa kungiyar Manchester United, ko kuma Roma, wanda dukannisu sun nuna sha'awarsu kan dan wasan.

Dan wasan gaba na Watford Richarlison, dan shekaru 21 na bukatar bin tsohon Kocinsa Marco Silva zuwa kungiyar kwallon Kafa ta Everton, inda ita kuma Kungiyar ta Everton ta fara tattaunawa da dan wasan gefe na kulob din Bordeaux's mai suna Malcolm, mai shekaru 21, da haihuwa a kan kudi fam miliyan 30.

Tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane, mai shekaru 46, a duniya zai koma kungiyar Juventus, a matsayin mai bada shawara a kungiyar,

Kocin dai ya buga wasa a kungiyar ta Juventus a shekara 1996 zuwa 2001 kafin ya koma kungiyar Real Madrid da taka leda daga bisani ya zamo Kocin na Real kafin ajiye aikinsa a bana. Inda ya samu nasarar lashe kofin zakarun turai sau uku a Jere wa kungiyar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG