Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Card Reader Raba Gardamar Zabe


INEC
INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta sanya ranar 7, ga watan Nuwamba, a matsayin ranar da za’a gudanar da zaben shugabanin kananan hukumomi da kansilolinsu a jihar Neja,

Kwamishinar yadda labarai a hukumar zaben Alhaji Muhammad Ahamad Agwara, ya bayana cewa hukumar ta kamala duk wasu shirye shirye da suka wajaba da tabbatar da cewa zasu yi amfani ne da naurar tantance masu jefa kuri’a, da ake kira “Card Reader.”

Tuni dai jami’yyun siyasa suka ce sun shiryawa shiga zaben sakataren babban jam’iyyar adawa ta PDP, a jihar Neja, Alhaji Aminu Yusuf, yace sun gamsu da matakan hukumar zaben amma suna fatan za’a bi doka.

Sai dai da alama jam’iyyar dake mulki a jihar wato APC, na fuskantar rikicin cikin gida a lokaci wannan zaben mai zuwa, Idris Usman Kontagora, wani jigo a jam’iyyar ta APC, yace basu da shakku a shirin hukumar zaben amma suna fargaba a cikin jam’iyyar su ta APC.

XS
SM
MD
LG