Accessibility links

Barcelona Da Real Madrid Na Fafatukar Lashe Gasar Laliga


A jiya kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, ta lallasa takwararta ta Celta Vigo daci 4-1 a gidan Celta a wasan da sukayi na laliga na shekarar 2016/17 mako na ashirin da daya wanda ya zamo kwantai a baya.

Wannan nasara da Real Madrid, ta samu ya bata damar darewa kan teburin laliga da maki 90 inda ta haura kan abokiyar hamayyarta Barcelona, wace take da maki 87 a matsayi na biyu.

A yanzu haka dai saura wasa daya yarage a kammala gasar ta laliga ta bana 2016/17. In har kungiyar Real Madrid ta samu nasara ko kunnen doki a wasan karshe to ta lashe gasar ta bana, in kuwa tayi akasin haka ita kuma Barcelona ta samu nasara a nata wasan to ita zata dauki gasar.

Ranar lahadi ashirin da daya ga watan mayu na shekara dubu biyu da goma sha bakwai kungiyoyin zasu buga wasan karshe inda Real zata je bakuncin gidan Malaga, Barcelona kuwa zata karbi bakuncin Eibar.

XS
SM
MD
LG