Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Banbancin makamashin nukiliya da makamin nukiliya


Shugaban Najeriya da tawagarsa yayinda jirginsu ya sauka a nan Amurka inda suka zo taron nukiliya
Shugaban Najeriya da tawagarsa yayinda jirginsu ya sauka a nan Amurka inda suka zo taron nukiliya

Masana a jami'ar Bayero dake Kano Farfasa Kamilu Sani Fagge da Dr Abba Fagge sun zanta da muryar Amurka akan taron nukiliya da kuma ita nukiliyar kanta

Idan ana batun makamin nukiliya galibi ana batun makamin nan na kare dangi to sai kuma ana batun makamashi daga nukiliya din wanda mutane da yawa basu da fahimta a kai.

Ana anfani da nukiliya a samu wutar lantarki ko makami. Hanya ta biyu ita ce ta samun bangaren da ake gina bam wanda karfinsa ya fi na kisan kare dangi hadari.

Ba za'a ce Najeriya bata da nukiliya ba amma ba ta hanyar gina bam din kare dangi ba ko kuma samar da wutar lantarki ba. Akwai sinadiran makamin nukiliya a makarantu kamar su jami'o'i da kwalajojin fasaha da kimiya da ake yin gwaje-gwaje domin a nuna wa dalibai yadda suke da yadda suke aiki.

Ganin irin illar da nukiliya ka iya jawowa tun daga lokacin yakin duniya da aka jefa bam a Hiroshima da Nakasaki a kasar Japan Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice ta ja kunnen duniya. Duk kasashen da suke dashi an fada masu kada su kara. Wadanda kuma basu dashi an haramta masu. Dalili ke nan duk kasashen dake yunkurin samun nukiliya sai kasashen duniya su yi masu ca saboda yarjejeniyar nan ta MDD.

Najeriya tana cikin kasashen da suka rabtaba hannu akan yarjejeniyar hana yaduwar makamin nukiliya amma ba makamashi ba. Akwai banbanci tsakanin makamashin da kuma shi makamin. Makamin shi ne ake anfani dashi wajen yaki da karkashe mutane. Makamashi kuma shi ne ake anfani dashi wajen kawo ayyuka irinsu lantarki da ma'aikatu daban daban na kirkiro fasaha. Yarjejeniya ta hana wanda za'a yi anfani dashi a samu makami ne wajen cutar da al'umma.

Kasancewar Najeriya a taron nukiliya zai taimaka domin kwana kwanan nan Majalisar Dinkin Duniya ta nuna goyon bayanta ga Najeriya wajen inganta wutar lantarki. Najeriya na iya cin gajiyar anfanin nukiliya wurin samar da wutar lantarki, wato a yarjewa Najeriya ta yi anfani da nukiliya da zummar samun wutar lantarki. Ana iya ba Najeriya fasahar yadda zata samu wutar lantarki ta yin anfani da nukiliya.

Ga karin bayani

XS
SM
MD
LG