Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Abin Da Ya fi Jajircewa A Nemi Na kai- Inji Umma Musa


Wahala da tsananin aikin kamfani ya tilasta ni dole barin aiki tare da neman aikin banki domin samun lokaci ga mai gidana da ‘yayana inji Umma Musa, kamar yadda ta bayyana wa wakiliyar DandalinVOA.

Ta kara da cewa kafin ta fara aikin banki sai da ta fara aikin kamfanin inda suke shafe awannin takwas suna aiki kuma akan kudi kalilan, duk kuwa da cewar aikin ban a azo a gani bane.

Umma ta bayyana cewa bata yi nisa a karatun boko ba, iya kacinta sakandare wanda hakan yasa bata sami wani aiki mai tsaoka ba sai dai leburanci wanda da shi ne take taimakawa mai gidanta da ma yaranta.

Kasancewar it ace shugabar masu goge goge ne ta ce wasu lokuta takan fuskanci matsala daga wajen abokan aikinta mussaamam ma maza, naganin ya za’ayi mace ta zama shugabarsu in ji Umma. Daga karshe ta ja hankalin mata matasa da su jajirce wajen neman nasu na kansu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:12 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG