Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Buri Na A Rayuwa In Taimakawa Al'umma Ta


A shirinmu na wasu muhimman mata da suka taka rawa a al'ummarsu a yau bakuncin malama Hadiza Muhammad Ali, muka samu matashiya mai sha'awar rubuce-rubucen labarai.

Hadiza Ali, dai ta ce ta fara rubce-rubuce tun tana makarantar sakandare , inda bayan kammala karatun ta samu gurbin karatu a Yola, inda ta karanci aiki lauya ta kuma samu takardar DIploma.

Daga nan bayan auren ta bai yi nisa ba ta dawo garin Kano inda aka yi fim da wani labarin da ta rubuta mai suna 'Rabo ajali' wanda ya fito a shekara ta 2014.

Ta ce bayan rubuce-rubuce tana da sha'awar aikin jarida wanda zuwa garin Kano ya bata damar shiga jami'ar Bayero ta Kano inda a yanzu take ajin karshen .

babban burin ta a rayuwa shine ta taimakawa al'umma wanda ko da bayan ranta za'a ce ga wani aiki da Hadiza Muhammad ali ta yi wa al'umma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:47 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG