Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Tuhumar Wasu 'Yansanda da Kisan Fulani Akan Abun Goro


Fulani makiyayi.
Fulani makiyayi.

Bisa wani zargin da ake yima wasu ‘yansanda a garin Tangwa yankin kudu a jihar Adamawa, da kashe wasu samari ‘yan Fulani su biyu. Ana dai tuhumar wadannan ‘yan sandar ne dacewar sun nemi wadannan ‘yan Fulani da subasu abun goro wanda sukuma matasan sukaki, wanda a sanadiyyar hakan yasa suka bindige su har lahira.

Ta bakin kakakin rundunar ‘yansanda a jihar ta Adamawa DSP Usman Abubakar, yace wadannan ‘yan sandan na tsare a shal kwatar rundunar ‘yansandar yanzu haka don gudanar da bincike, wanda anasa ran idan aka samesu da wani laifi za’a gurfanar dasu a gaban kuliya. Ya kuma kara da cewar yanzu haka wasu manyan jami’an hukumar ta ‘yansadan na gudanar bincike a kan lamarin, ya kuma yi kira da jama’a suyi hakuri kada su dauki hukunci a hannunsu. Za kuma a bayyanar da rahoton wannan binciken nan ba da dadewa ba.

Ita kungiyar kare hakin makiyaya ta kasa baki daya wato Kungiyar Miyatti Allah, ta nuna rashin jin dadinta akan abubuwan dake faruwa tsakanin makiyaya da ‘yansanda, a cewar jami’in tuntuba na kungiyar Mal. Sanusi Bara, kungiyar ta bada umurni cewar kada wani bafullatani ya sake bama kowane dansanda cinhanci, saboda wannan abun goron da suke basu yazama sun maida Fulani wani hanyar kasuwanci, adalilin haka yasa sukace babu wanda zai sake basu wani abu. Kuma kungiyar tana iya bakin kokarinta don ganin ta kare ma makiyayan hakokinsu a kowane mataki.

Shima Alh. Umaru Dan-Kano shugaban kungiyar kafofin yada labarai a jihar ta Adamawa, ya nuna takaicin yadda abubuwan ke faruwa, wanda yace yakamata hukuma da duk wadannda abun yashafa suyi kokarin daukar mataki da yakamata, sukuma al’ummah su kai zuciya nesa don ganin an samu zaman lafiya baki daya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG