Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Iya Kamuwa Da Cutar Zika Ta Wajan Cizon Sauro Da Juma'i


Nau'in sauron da ke yadad zazzabin shawara har ila yau shi ke yada cutar ZIKA dan haka idan mutum bai kula ba sai ya dauka ko ya kamu da zazzabin gama gari ne kawai ba Zika da kan kawo tawaya a girman kwallon kan jariri da kwakwalwarsa ba.

A yanzu haka dai hukumar lafiya ta duniya ta yi kira domin neman daukar matakin gaggawa a kan lamarin da a yayi sanadiyyar haihuwar yara da dama masu dauke da wannan larura musamman a kasar Brazil da wasu kasashe a kewayen.

Dan haka ne kwararren likita Dr Disu ya yi kira musamman ga mata masu juna biyu da su guji kai ziyara zuwa kasashen Latin Amurka inda cutar ta fi kamari a yayin da suke da ciki da kuma lura domin kaucewa cizon sauro idan tafiyar ta kama dole.

Gabanin wani rahoto da ya nuna cewar ana iya daukar cutar ta hanyar juma'i, lamarin yazo a daidai lokacin da Najeriya ke fama da annobar cutar Lasa da bera ke yadawa.

Saurari cikakken rahoton a nan...Dandalinvoa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG