Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karkashin Kasa Na Iya Zama Asusun Ajiyar Kayan Tarihi


Gunki
Gunki

A cikin irin bincike da ake cigaba da gudanarwa a kasar Egypt, an sake samo wani mutun-mutumin katako da aka sassaka na wata mata. Masanan dai sun bayyanar da wannan gunkin a matsayin matar sarki Pharaoh Amenhotep lll, wanda yayi zamani daga shekarar alib dubu daya da dari uku da casa’in da daya 1391 zuwa alib dubu daya da dari uku da hamsin da uku 1353, kamin bayyanar annabi Isah (A.S).

An dai tsunto wannan gunkin ne a garin Luxor, dake da tarinhin mutanen da. A cewar Mr. Sultan Eid, darakta a ma’aikatar binciken arzikin kasa, yace wannan gunki da aka gano na rataye da filawa, da wasu abubuwan hannu masu kala-kala, haka da wata sarka, ya kara da cewar wannan gunkin ya samu wajen ajiya mai kyau domin kuwa baiyi komai ba, kuma an kiyasta shekarun wannan mutun-mutumin zai kai shekaru dari biyar 500. Hakan dai ya kara sa su cigaba da bincike don gano idan akwai sauran abubuwa da akayi amfani da su a zamanin annabawa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG