Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Horar Da Karnuka Sunsuno Yanayin Sukari a Jikin Bil'adama


Ana iya horar da karnuka yadda za su sunsuna miyagun kwayoyi ko nakiyoyi, a saboda haka Mark Ruefenacht ya yi tunanin yiwuwar yin amafani da basirar da dabbobin ke da ita ta sunsuna abubuwa don gano sauyin yanayin sukari a jikin bil’adama.

Ruefenacht yayi aiki da wasu kwararru a fannin kimiya ya kuma dauki nauyin binciken da ya gano cewa ana iya sunsuna gahin karancin sukari a jinin bil’adama ta numfashinsa da kuma zufa. Ya kuma yi aiki tare da duba yadda kwararru ke horar da karnuka yadda za su iya sunsuno kama daga nakiyoyi har zuwa cutar sankara. Daga nan Ruefenacht ya fara horar da wani dan kare da ya sawa suna Armstrong yadda zai nuna mashi alama a duk lokacin da sukarin jikinsa yayi kasa fiye da kima. Kuma ya yi nasara wajen horar da karen, saboda Armstrong ya shiga litafin tarihi na duniya a matsayin karen farko da ya gano cutar sukari.

Ko da yake Armstrong ya mutu, Ruefenacht ya bude wani kamfanin horar da karnuka da ake kira Dogs4Diabetics. Ya kuma ce horar da kare gano yanayin sukari da mai karen, zai kai dala 50,000. Ta haka Kamfanin ke samun kudaden gudanarwa, da kuma bada karnukan ga mutanen da suka cancanta kyauta.

Ana horar da karnukan yadda za su sunsuno yanayin karancin sukari a jikin bil’adama a ko da yaushe. Ruefenacht ya yi amfani da wasu kwalabe dake dauke da dugon zufar mai cutar sukari, wanda yanayin sukarin cikin jininsa ta yi kasa, tare da wasu kwalaben dauke da abubuwa masu kamshi dabam-dabam kamar markadaddar gyada, ko abincin kare. A duk lokacin da karnukan suka gano kwalbar zufar akan basu kyauta. Kuma binciken kimiya ya tabbatar da ingancin wannan horon.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG