Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Mata 'Yan Kasar Sin Masu Karuwanci a Najeriya


Hukumar shige da fice ta Najeriya ta kama wasu ‘yan mata 13, 'yan kasar Sin masu aikin karuwanci a Ikeja, ta Jahar Lagos.

Su dai wadannan ‘yan mata an kama sune a lokacin da ma’aikatan shige da fice suka kai wani sumame a dabar su dake Ikeja.

Rahotani sun ce masu fada aji da ‘yan siyasa da turawa ne ke ma’amala da wadannan ‘yan matan su kan kuma biyansu tsakanin Dala Amurka 1.000 zuwa 2.500,

Wani 'dan asalin Sin, mai suna Sun da matarsa Yin Li, ne ke gudanar da wannan aikin masha’a , Kuma suna da ‘yan mata fiye da ‘yan mata 40, da suke gudanar da wannan muguwar sana’ar dasu.

Shi dai Sun da matar sa Yin Li, da sauran ‘yan matan sun samu sun ranta a na kare a lokacin da jami’an shige da fice suka farwar gidan nasu dake Ikeja.

XS
SM
MD
LG