Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fitar Da Jadawalin 'Yan-Wasan Najeriya Da Zasu Kara A Afrika Ta Kudu


Mai horas da tawagar 'yan wasan Super Eagle dake tarayyar Najeriya Gernot Rohr, ya fidda jaddawalin jerin sunayen 'yan wasan da zasu fafata a wasan da Najeriya zata yi tsakaninta da kasar Afirka ta kudu, a Johannesburg na neman cancatar shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika da za'a yi a 2019.

Sai dai a wannan Karonma babu sunan jagoran 'yan wasan wato Mikel Obi cikin jerin sunayen 'yan wasa 23 da kocin ya fitar inda wasu ke ganin hakan wata alamace ta shirin kawo karshen wasan Obi a wasan kasa da kasa.

Mikel Obi wanda tsohon dan wasan Chelsea ne wadda yanzu yake taka Leda a wata kungiya dake kasar Sin, bai samu damar shiga jerin 'yan wasan Najeriya ba da suka buga wasanni har guda biyu na neman tikitin shiga gasar ta nahiyar Afrika inda Najeriya ta doke Libya da ci 4-2 a gida da kuma 3-2 a waje.

A wasan da Najeriya zata fafata da kungyar Bafana Bafana ta kasar Afirka ta kudu, ya kasance manyan 'yan wasa uku na Najeriya irin su Victor Moses da ya ajiye takalmansa wa kasarsa da Mikel Our, sai kuma Wilfred Ndidi.

Jerin sunayen da kocin Gernot Rohr ya fitar sun hada da masu tsaron raga

Daniel Akpeyi na Kungiyar Chippa United‚ A Afirka ta kudu)‚ da Ikechukwu Ezenwa (Enyimba Nijeriya) sai Francis Uzoho daga kulob din (Elche‚ na Spain).

Sai masu tsaron baya. Ola Aina na Torino‚ Itali)‚ Semi Ajayi (Rotherham United‚ a Ingila )‚ Adeleye Aniyikaye (IfenayiUbah)‚ Leon Balogun
(Brighton and Hove Albion‚)‚ Jamilu Collins (Paderborn‚ William Ekong
Troost (Udinese‚ Itali)‚ Bryan Idowu (Lokomotiv Moscow‚)‚ Kenneth
Omeruo (Leganes‚ dake Spain).

A bangaren 'yan wasan tsakiya kuwa akwai, Mikel Agu (Vitoria Setubal‚ Portugal) Oghenekaro Etebo (Stoke City) John Ogu (Hapoel Be'er Sheva‚ Israel).

Daga bangaren masu jefa kwallo kuwa sun kunshi, 'yan wasa kamar haka, Amuel Chukwueze (Villarreal‚ Spain)‚ Odion Ighalo (Changchun Yatai‚ Sin)‚ Kelechi Iheanacho (Leicester City)‚ Alex Iwobi (Arsenal‚ Samuel Kalu
Girondins Bordeaux‚ Faransa )‚ Ahmed Musa (Al Nasr‚ Saudi Arabia)‚ Victor Osimhen (Charleroi‚ Belgium)‚ Moses Simon (Levante ‚ Spain)‚ Isaac Success (Watford).

Wasan zai gudanane a cikin watan Nuwamba mai zuwa a Johannesburg, babban birnin Afrika ta kudu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG