Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abdullahi Isa: Har Yanzu Ba a Ba Matasa Damar A Dama Dasu Ba


A Siyasar Najeriya, muddin dan takara bashi da kudin kashewa, zai yi wahala ya taka wata muhimimiyar rawa.

A cikin shirin mu na matasa da siyasa DandalinVOA ya samu bakuncin wani mai sharhi kan al’ammuran yau da kullum na matasa malam Abdullahi Isa, wanda muka zanta da shi akan harkokin siyasar matasa a Najeriya, kuma yayi hasashen cewa har yanzu ba a ba matasa damar damawa dasu a harkokin siyasa.

Batun ko ana damawa da matasa a harkar siyasa batu ne da aka jima ana fafatawa, idan aka yi waiwaye dangane da kudirin da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sanya hannu na "Not too young to run" ba ita ce kadai matsala ba a harkar siyasar matasa a Najeriya ba, illa batu ne na kudi.

Ya ce siyasar Najeriya, muddin dan takara bashi da kudin kashewa, zai yi wahala ya taka wata muhimimiyar rawa, Idan har anason a samu gudunmuwar matasa a siyasar kasar sai mutane sun cire son duniya daga zukatan su.

Daga karshe ya yi kira ga 'yan Najeriya, da su san muhimmancin 'yancin su da yaki da cin hanci da rashawa tsakaninsu, da zabar 'yan takarar da suka cancanta ta wannan hanyar ne za’a samu cigaban da ake bukata a demokradiyar Nijeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG