Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karo Na 5 Kungiyar AMMA Zata Karrama Gwarzaye


Bashir Yusuf
Bashir Yusuf

Bashir Yusuf daya daga cikin jigo na shiryawa da bada kyautar girma ta “AMMA- Award” wato 'Arewa Music and Movie Award Karo” karo na 5, wanda yake cewar, kimanin mawaka 18 da ‘yan wasan finafinai 23 ne zasu sami damar lashen kambun girmamawa na AMMA Award da za’a gudanar a jihar Katsina.

Bashir Yusuf, ya ce wannan shine karo na 5, wanda za’a gudanar da taron walima a jihar Kano, inda za’a bada takardar shaida ga wasu daga cikin wadanda zasu karbi lambar girmamawan.

Ya ce kawo yanzu dai an sami cigaba da yadda ake bada lambar girmamawa, inda suke duba da yadda ‘yan masana’antar ke shiga gasar tare da baiwa abun muhimmaci, sabbani yadda ake yi a da, inda mafi yawan lokutan basa cike ka’idoji na finafinai yadda ya kamata.

Ya kara da cewa a wannan karon, sai da mawaka da jarumai ko ‘yan kungiyar Kannywood suka biya wani hasafin kafin su sami damar shiga rukuni-rukuni na karramawar domin samun damar a zabe su.

Bashir Yusuf, wanda yana daga cikin wadanda suke da alhakin kula da shirin ya ce kawo yanzu dai, gwamnatin jihar Katsina ce kadai ta ba da tallafi tare da marawa shirin baya domin ganin an gudar da shi cikin lumana.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG