Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadar White House Na Tsananta Bincike Akan Shafufukan Yanar Gizo


Shugaban Kamfanin Facebook Mark Zuckerberg
Shugaban Kamfanin Facebook Mark Zuckerberg

Taron matasa mazu hazakar sarrafa kimiyya da fasaha, sun gudanar da wani taro, da zummar fito da hanyoyi da za’a inganta kafafen sada zumunta, na yanar gizo ‘social media’ a turance. Babban makasudin taron shine, hanyoyi da za’abi wajen ganin an inganta tsaro a shafufukan yanar gizo.

Wannan taron ya banban ta da irin wadanda akeyi a baya, ganin yadda duniya ta saka ido a kafofin shafufukan yanar gizo, kodai wajen yada labarin gaskiya, ko na kanzon kurege.

A wajen taron, shugaban shahararren kamfanin facebook, ya bada tabbacin cewar, zasu bama ‘yan majalisar dokokin kasar Amurka, kundin ajiyar bayanai na kamfanin, don su gudanar da bincike, akan alakar gwamnatin kasar Rasha da irin kutse da ake zargin sunyi a zaben kasar da aka gabatar a shekarar da ta gabata.

Za suyi duba a duk wasu tallace-tallace da aka buga a shafin, wanda bayyamar da ra'ayin gwamnatin kasar Rasha da zaben kasar Amurka.

A cewar shugan kamfanin Mark Zuckerberg, “Muna cikin sabuwar duniya” wannan wani bakon al’amari ne, kuma kalubale ne ga duniyar kimiyya da fasaha, ganin yadda wasu kasashe ke shiga harkar da ta shafi wasu kasashe, wajen bada gudun mawa ga tsarin zaben wasu kasashen.

Don haka idan akwai bukatar mu bada gudunmawa don kaucema aukuwar haka a gaba, to babu shakka zamuyi hakan. Yanzu haka mahukunta na ganawa da zakakun matasa, a fannin kere-keren duniyar kimiyya da fasaha, a babban birnin tarayyar Amurka.

Matasan sun bayyanar da kimiyya da fasaha, a matsayin wata hanyar da jama’a ke iya bayyanar da ra’ayoyin su, batare da wata tsangwama ba, don haka wannan dama ce da ta kamata ayi amfani da ita ta hanyar da ta kamata, don cinma burin duk wata dama a rayuwar dan’adam.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG