Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mawaka Ba Mutanen Banza Bane, Suna Gyaran Al'umma


Mubarak Nuhu Alhasan MK
Mubarak Nuhu Alhasan MK

A shirinmu na nishadi a yau, mun sake samun zantawa da Mubarak Nuhu Alhasan (MK). Mawakin hip-hop wanda ya shafe shekaru yana yi, ya kuma fitar da wata wakarsa mai suna ‘Talatu' wakar da ya rera ba tare da ya rubuta ta ba ko me yasa.

MK ya ce ya fara sha’awar waka ne sakamakon yawan jin wakokinsu, mawaka namu na gida irinnsu 'Billy O' wanda shi ne gwarzonsa, sanadiyarsa ne ya fara waka.

Ya ce wakar 'Billy O' mai take 'Ban Kudin Tuba’ na daya daga cikin wakokin da suka ja hankalin shi, kuma ya shafe kamar shekaru takwas kenan yana waka, inda ya samu damar rera waka da gwarzonsa a wata waka ta ‘Sardauna Bahago dan Hassan’

Ya kara da cewa, wakar Talatu ita ce karon farko da ya rera waka ba tare da ya rubutu ba. Kamar yadda akan ce yau da gobe ta wuce wasa, yana shiga studio sai baitocin suka rika zuwan masa kamar wahayi.

Sannan ya ce yana waka ne da zummar fadakarwa da kuma nishadantar da masu sauraro.

MK, ya ce babban kalulabe shine, yadda ake yiwa mawaki kallon dan iska, sakamakon wadanda suka fara waka a da, akan alakantasu da rashin tarbiya da kuma akasari a wancan lokaci suna waka ne a gidajen bariki.

MK, ya kuma ce yana fata a gaba zai dinga sirkawa, da yin wakokin da zarar basirar sun zo masa a kwakwalwa ba tare da ya rubuta su ba. Babban burin shi ya wuce ya cigaba a harkar waka har duniya ta sanshi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG