Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sama Jannatin Amurka Da Rasha Sun Sauka Bayan Watanni Shida


Jerin ‘yan sama jannatin kasar Amurka da Rasha su uku, sun sauka a wannan duniyar, bayan kwashe watanni shida a sararrin samaniya. Masanan da suka tafi duniyar watan don bincike, sun sauko ta hanyar amfani da kunbo afolo.

Sun baro duniyar wata da misalin karfe 4:00am na safe, sun sauka a kasar Kazakhstan, da karfe 7:20am na safe. Wanda ya daukesu kimanin tafiyar awowi uku da rabi.

A cewar matukin kunbo afolon, Komanda Shane Kimbrough, dan asalin kasar Rasha, “Babu abun jin dadi da ya wuce ace mutun yayi irin wannan tafiyar, don zuwa wata duniya. Ko dai babu komai wannan tafiyar tafi karfin su, sai dai a hada ta da karfin kasa baki daya”

Ya kara da cewa, a ziyarar aiki da suka kai duniyar wata, sun gamu da wasu abubuwa da basu taba tunani ba, wanda kuma suke da matukar muhimanci ga rayuwar dan’adam.

Masanan guda uku dai, sun tafi wannan binciken da aka ware ma makudan kudade dallar Amurka billiyan dari. Nisan tafiyar da sukayi a sararrin samaniya ta wuce nisan kilomita dari hudu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG