Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Facebook Da Maidakin Shi, Suna Shirin Karbar Sabuwar Jaririya!


Shugaban Kamfanin Facebook Mark Zuckerberg da mai dakin shi Priscilla Chan,
Shugaban Kamfanin Facebook Mark Zuckerberg da mai dakin shi Priscilla Chan,

Shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg, da maidakin shi Priscilla Chan, suna tsammanin sabuwar jaririrya. Kimanin shekara daya kenan da ta wuce, suka haifi yarinya mai suna Max.

Mark ya rubuta a shafin shi na facebook cewar, matar shi tana da juna biyu, suna kuma cike da farin cikin samun karuwa a dangin su, wanda suke sa ran haihuwar wata jaririryar.

Ya kara da cewar shima ya tashi a tsakanin ‘yan mata uku, itama matar shi tana da yayyi biyu. Ya bayyanar da yayyin shi mata a matsayin wadanda suka koya mishi abubuwa da dama da yanzu yake cin gajiya. Duk basirar shi tana da nasaba da gudunmawar su.

Haka itama matar shi mafi akasarin cigaban da ta samu a rayuwa, yana da nasaba da yadda yayyin ta mata suka koya mata abubuwa, a lokacin yarintar ta. Zama tsakanin ‘yan mata wata baiwa ce ga duk wani yaro, a lokacin yarinta. Suna dai cike da farincin na wannan sabuwar jaririryar, da za’a haifa nan bada jimawa ba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG