Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dimamar Yanayi A Fadin Duniya, Zai Shafi Rayuwar Bil'adama!


Dimamar Yanayi
Dimamar Yanayi

Bincike da aka zurfafa, ya bayyanar da yadda dumaman yanayi ke harzuka karfin wuta a cikin dokar daji. Tsangayar bincike kan harkar kimiyya, sun bayyanar da cewar, kimanin karni uku da suka gabata, an kara samun hauhawar karin gobara a cikin dazuzuka, wanda hakan yake da alaka da zafin yanayi tun daga shekarar 1984 zuwa yau.

Binciken ya maida hankali ne wajen yadda kasa ke bushewa, musamman a cikin dokar daji. Wanda suke hasashen hakan a sanadiyar karuwar gobara, a kowane lokaci ta taso a dokar daji. Kimanin kashi hamsin da biyar 55% na ruruwar gobara a daji na haddasuwa ne, akan yadda itatuwa ke bushewa saboda zafi, a sanadiyar rashin samun ruwan sama akai-akai.

Tsangayar binciken yanayi a jami’ar Idaho ta nan kasar Amurka, da jami’ar Gundumar Kwalambiya, sun tabbatar da cewar, mutane suke haddasa bushewar dazuzuka, wajen amfani da kayan zamanin da suke haifar da guba ga tsirrai.

A karshe sun hasashi cewar, idan ba’a dauki matakai da suka dace ba cikin gaggawa, wannan annobar ta konewar gandun daji, zata cigaba, kuma zata iya zama musiba, ga jama’a a nan gaba kadan.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG