Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kirkiri Wani Sabon Mutunmutumi Abokin Kowa, Babu Abun Da Bayayi!


Mutunmutumi Abokin Kowa
Mutunmutumi Abokin Kowa
Masana na cigaba da zurfafa bincike wajen maida mutun-mutumi “Robot” tamkar mutun, shahararren kanfanin kera robot na kasar China, sun kirkiri wani sabon mutun-mutumi, da suka sama suna “Nxrob”, da yake mu’amala da mutane kamar yadda mutane, suke gabatar da zaman takewar su a tsakanin jinsin dan’adam. Shi dai sabon mutun-mutumin yakan gabatar da duk wasu abubuwa, da mutun kanyi a gida, kamar kunn talabijin, kunna na’urar dimama daki, da sanin irin yanayin da ya kamata mutun ya zauna a cikin daki, yana fira da mutun don bashi labarin dariya da abun ban mamaki. Haka mutun mutumin, ya kan yi wasa da yara, da tunamusu wasu abubuwa da yakamata ace sunyi, a kowane lokaci a rana, yakan tunama yaro cewar an bashi aikin gida daga makaranta, don haka sai ya kokarta wajenyi. Bai tsaya nan kawai ba, yana da basirar sanin kowane mutun da yake cikin iyalan gida, da irin abun da kowane mahaluki yake bukata, kamar irin kalan kayan da mutun yake so, kana da irin abincin da mutun yafi so. Haka idan dakin mutun yayi sanyi ko zafi, bayan mutun na bacci, roboto din ya kan sauya yanayin dakin wajen kunna na’urar da zata maida dakin wajen zama, batare da wata matsala ga lafiya mutun.
  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG