Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aljanin Sama Jannati "Drone" Zai Kara Karfafa Tsaro Cikin Awowi 24/7!


Aljanin Sama Jannati "Autonomous Drones"
Aljanin Sama Jannati "Autonomous Drones"

Wasu matasa sun kirkiri aljanin Sama Jannati “Drone” wani sabon tsarin aljanin da suka kirkira yana da banbanci da saura. Domin kuwa wannan yana aiki kamar mai tsaron gida, na tsawon sa’o’i ashirin da hudu, kwanaki bakwai cikin mako.

A cewar jagoran tawagar matasan Mr. Ariel Avitan, sun kirkiri wannan Aljanin Sama Jannatin, dauke da abubuwa da dama, wanda su kayi amfani da hotuna sama da milliyoyi, wajen koyama aljanin yadda zai iya gane mutun ko motsin wani abu daga sararrin samaniya. Musamman idan akwai alamun rashin gaskiya.

Komin duhun dare, idan akwai wata alamar rashin gaskiya, aljanin zai iya ganewa, kuma zai dauki hoto da bidiyon abun da ke faruwa, haka zai aika da sakon gaggawa cewar ga abun dake faruwa a yanki kaza.

Aljanin yana dauke da kyamarori masu yawa, yana kuma da wuya mutun ya iya ganin shi a lokacin da yake cikin sararrin samaniya. Aljanin saman yana cin gashin kanshi a yayin shawagi a cikin sararrin samaniya, batare da wani yana bashi umurni ba, zaiyi aiki na tsawon shekara daya batare da hutawa ba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG