Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ilimin Addini Da Na Zamani Sune Maganin Zaman Takewa A Tsakanin Jama'a!


Solomom Timothy
Solomom Timothy

Solomon Timothy Anjide, matashi dan Najeriya ne dake karatun Digirin digirgir a fanin binciken zaman lafiya, da kwanciyar hankali a tsakanin al'uma. A Jami'ar Lincoln dake kasar Birtaniya. Yayi karin haske dangane da irin binciken da yake gudanarwa da ya shafi zaman lafia.

Neman ilimi, don iya zaman duniya, yasa ni bincike a wannan fanin na yaki ta ta’addanci da kawo zaman lafiya cikin al’uma. Solomon, yana fatar idan Allah yasa ya kammala karatun shi, ya koma gida Najeriya don cigaba da bada tashi gudunmawa ga matasa.

Babban taimako da matasa za suyi ma kansu shine, su tashi tsaye wajen neman ilimi, wadanda kuma suke harkara kasuwanci, sai su maida hankali matuka, kuma su dinga neman shawarar sauran abokan su, da sukayi karatu don su zamanantar da kasuwanci na su.

Solomon ya yarda cewa waddanan abubuwa uku sune kashin bayan zaman lafiya da ci gaban ko wace al’umma. Ya kuma yarda cewa Allah ya bama kowa baiwa da basira, kuma wajibi ne matasa su nemi ilimin Boko da na addini don samun kaifin basira, domin yin sana’a da kuma wanzar da kyakyawan zamantakewa da kuma ma’amala.

Bisa ga abin da Solomon ya gani wa idon sa, a kasar Birtaniya, Solomon na kiran ‘yan-uwa shi matasa, su hada kai wurin samar da kamfanoni a tsakanin su. A karshe Solomon, yana mika sakon gaisuwa, da kuma fatan alheri ga duka matasan Najeriya, a ko ina suke. Allah ya taimake mu baki daya, kuma ya taimaki kasar mu baki daya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG