Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Sun Gano Wani Magani, Mai Kara Basirar kwakwalwa!


Tsakiyar Kwakwalwar Dan'adam
Tsakiyar Kwakwalwar Dan'adam

Taron masana binciken kwakwalwar dan’adam a garin “Silicon Valley” dake jihar California, ta kasar Amurka, sun gabatar da wani bincike, da ya bayyanar da cewar, mafi akasarin mutane a fadin duniya, kanyi amfani da kashi goma sha biyu 12% ne kawai na kwakwalwar su.

Hakan yasa suka kirkiri wani magani, da yake taimakama mutane da suka sha wajen budewar kwakwalwa, wanda idan mutun ya sha maganin, zai taimaka mishi wajen bude kwakwawalr, mutun tayi aki a cikakken mataki da ya kamata ace kwalwalwa na aiki.

Duk mutumin da ya sha maganin, maganin zai taimaka ma kwakwalwar shi, wajen bude sauran kashi tamani da takwas 88% wanda zai cike dari bisa dari 100%. A cewar Dr. Raqif, wannan maganin da suka kirkira mai suna “EnhanceMindIQ” yana tada jijiyoyin dake kwakwalwar mutun don basu damar da ya kamata suyi aikin su yadda ya kamata.

Yanzu haka dai mutane da dama basu yadda da aikin wannan maganin ba, duk dai da hakan matasa ‘yan makaranta suna ta siyan maganin don gwaji. Ana dai shan maganin ne a tsawon sati hudu, wanda kwakwalwar mutun zata dinga aiki ba kama hannun yaro. Kwalbar maganin takan kai kimanin dallar Amurka dari uku $300 dai-dai naira dubu dari da ashirin.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG