Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paul Pogba Ya Lashe Kyauta A Manchester United


Dan wasn tsakiya na kasar faransa mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, mai shekaru ashirin da uku a duniya Paul Pogba, ya lashe kyautar dan wasan da yaci kwallon da tafi kowace kwallo kyau a watan Oktoba da ya wuce a kungiyar Manchester United (MUFC Goal of the Month )

Pogba ya samu wannan nasaranne a wasan da kungiyar ta Manchester tayi da takwararta ta Fenerbahce ranar ashirin ga watan oktoba 2016, a gasar cin kofin Yurofiyan lig, na bana inda Manchester ta samu nasara akan su daci 4-1.

Pogba ya samu damar jefa kwallaye har biyu a ragar Fenerbahce inda ya zura kwallonsa ta farko a cikin mintuna 32, da fara wasa daga bisani ya sake jefa ta biyu a mintuna na 45.

A yanzu haka Pogba ya jefa kwallaye hudu kacal a Manchester United tun zuwan sa na farkon kakar wasan bana.

Yanzu haka shi ke kan gaba a wajan tsadar 'yan wasan kwallon kafa a duniya akan zunzurutun kudi har fam miliyan £89.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG