Shahararren dan tseren duniya, Usain Bolt, dan asalin kasar Jamaica. Wanda ya zama zakaran gwajin dafi a fagen tsere a duniya. Ya samu damar lashe tagulla tara 9, a wasannin Olympic tara 9.
Ya bayyanar da cewar idan Allah, ya kaimu shekara mai zuwa, zai yi wasan shi na karshe, wanda ake sa ran za’a yi a kasar Birtaniya. Dan tseren Bolt, mai shekaru talatin 30, da haihuwa ya tabbatar da cewar a shekarar, mai zuwa yake sa ran zaiyi tseren karshe, inda yake sa ran zaiyi shi a gaban ‘yan kasar shi, a kasar ta Jamaica.
A tarihin dan tseran Bolt dai, ya samu damar lashe tseren mita dari 100, da na mita dari biyu 200, sai tseren mita dari hudu a karo uku a jere. Haka kuma ya zama dan tsere da ya kwashe tsawon shekaru goma sha daya 11, a jere a jere, yana rike da kambun dan tsren da yafi kowa gudu a fadin duniya.
A shekarar 2008 inda ya kammala tseren a cikin minttoci sha tara, da dakika talatin 19.30 haka a shekarar 2009 ya kammala a cikin minttoci sha tara da dakika shatara.