Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nuhu Dan-Mahawayi: Koyon Tukin Jirgin Sama, Nada Sauki Idan Mutun Yanada Hazaka!


Nuhu Khalil Dan-Mahawayi
Nuhu Khalil Dan-Mahawayi

Matashi Nuhu Khalil Dan-Mahawayi, an haife shine a kauyen Dan-Mahawayi, a karamar hukumar Giwa, Jihar Kaduna. Ya fara karatun ne a kwalejin koyon tukin jirgin sama dake Zaria, bayan kammala karatun firamari da sakandire duk a garin Zaria. Daga nan ya samu damar komawa kasar Afrika ta kudu, don karasa karatun shi na zama cikakken matukin jirgin sama.

Wanda a yanzu haka ya samu takardar “Private Pilot Licence” wanda aka tabbatar da cewar, zai iya tuka jirgin sama dauke da fasinjoji. Ya kuma samu damar kammala jarabawar da zata bashi damar tuka jirgin sama a tsakiyar dare.

A yanzu dai yana kokarin samun shaidar zama, kwararren matukin jirgin sama na ‘yan kasuwa, “Commercial Pilot Licenses” Wanda daga nan sai mutun ya fara karbar albashi. Babban kalubale da mafi akasarin matasa kan samu, wajen rashin karatun tukin jirgin sama shine, kudin makarantar na da matukar tsada, wanda ba kowa ne zai iya biya ba.

Abu na biyu kuwa shine, sai mutun ya maida hankalin shi matuka, wajen karatun da samun kamala jarabawar da ake gabatarwa, a kowane karshen zango. Domin kuwa sai mutun ya samu maki saba’in da biyar 75%, kamin ya samu damar zuwa aji nagaba.

A karshe yana kira ga ‘yan-uwan shi matasa, da su maida hankali wajen karatu, musamman idan suna da sha’awar karatun tukin jirgin sama, don karatu ne da baya tafiya da raggo. Amma karatune wanda yake da sauki, musamman idan mutun yana da ra’ayi a karatun.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG