Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashe Masu Tasowa, Ba'a Barsu A Baya Ba, Wajen Amfani Da Mutun-Mutumi!


Mutun-Mutumi
Mutun-Mutumi

Alamu na kara nuni da cewar, nan gaba kadan mutun mutumi “Robot” zai maye gurbin mutane a wajajen ayyuka da dama, bama kawai a kasashen da suka cigaba ba kawai, harma da kasashen da ke tasowa. Akwai bukatar kowane matashi ya kirkiri wata sana'a da zata kai babu bukatar amfani da mutun-mutumi.

A kasar Philippen, wasu matasa sun samar da wani kamfani da suke ayyuka, da dama da suka hada da daukar ma’aikata na wasu kamfanoni da samar da dangantaka tsakanin kamfanoni ta hanyar magana da ma’aikata wanda ake kira “customer care” a turance. Don biyan bukatar al'umah da tafiyar da rayuwar yau da kullun cikin sauki.

Yanzu haka kamfanin ya fara amfani da mutun-mutumin wajen gudanar da wadannan ayuyukan, wanda hakan zai sa milliyoyin mutane rasa aikin yi. Sai dai ana ganin cewar idan mutane za suyi amfani da irin baiwar da Allah, yayi musu, wajen kirkirar wasu sana’o’I da wasu ba suyi, ko ba’a gabatar dasu dan amfani da mutun-mutumi ba. Domin akwai wasu sana’o’I da sai mutun mai motsi kawai zai iya gabatar da su. Ta haka ne kawai za'a iya gujema rashin aikinyi a tsakanin matasa, nan da wasu shekaru kadan masu zuwa

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG