Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

RIO 2016: 'Yan-Wasan Najeriya Sunsha Kaye, Amma Suna Da Dama A Gaba!


Kwallon Raga
Kwallon Raga

‘Yan wasan Najeriya a bangaren kwallon raga “Basket Ball” cikin wasannin Rio Olympics, sun sha kashi a hannun ‘yan wasan kasar Brazil, inda aka tashi da maki 86-69. Wanda hakan ya basu damar shiga wasan zagayen kusa da karshe.

Dan wasa Jazz, ya samar musu da maki biyar da kuma bada damar da yasa ‘yan wasan Brazil suka tserema abokan wasan suna Najeriya. Shi kuwa dan wasa Neto, ya rike gida sosai duk dai da cewar bai samu damar buga wasa da ‘yan Najeriya ba.

Ana dai sa ran ‘yan wasan Najeriya, zasu sake gwabza wasa a wani zagaye, wanda idan su kayi nasara, zasu samu damar shiga cikin zagayen kusan karshe, daga nan sai wasan karshe.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG