Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Tantama Akan Shekaru Renato Sanches


Renato Sanches
Renato Sanches

A ci gaba da gasar nahiyar Turai,da ake yi a kasar faransa za’a ci gaba da wasan kusa da na karshe tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Wales, da kasar Portugal.

Mai horas da ‘yan wasan Portugal, Fernadez Santos, dan shekaru sittin da daya ya fito fili yak are dan wasan Portugal mai suna Renato Sanches, dan shekaru goma sha takwas mai bugawa kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, wanda ake zargin sa da rage shekarun san a haihuwa.

Shi dai wannan dan wasan,wani tsohon mai horas da wasan kwallon kafa kimaninshekaru arba’in baya kuma dan kasar Faransa, mai shekaru saba’in da bakwai mai suna Gay Rock, ne ke zargin cewa an rake shekarun haihuwar Sanches,

Yana mai cewa yakamata ace shekarun Sanches ashirin da uku ne ko kuma da hudu domin duba dayadda yake taka leda.

XS
SM
MD
LG