Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwallon Kafa Ta Mexico Ta Dakawa Najeria U-23 Kashi


Wasannin shirye shiryen Rio Olympic da ake dab da farawa, jiya Kungiyar kwallon kafa ta Mexico ta dakawa takwararta ta ‘yan kasa da shekaru 23 ta Njeriya kashi da ci 1 – 0 a filin wasan Estadio Victoria.

Dan wasan Mexico mai suna Marco Bueno ne ya sami nasarar jefa kwallo a ragar Najeriya cikin minti na 65 da fara wasan, yayin da ya zare kwallon daga ‘yan wasan gaba na Najeriyar sa’annan yaba dan tsaron gida Emmanuel Daniel mamaki.

Kungiyar kwallon kafar Mexico ce ta marabci wasan kuma kungiyar ce ta lashe kyautar Gwal ta wasannin kwallon kafa na Olympic da aka buga a London shekaru 4 da suka gabata.

Kungiyar ta yi ta kai kora inda suka kusa jefa wata kwallon a cikin mintuna na 83, da farkon rabin lokaci dai wasan ya tashi ne babu kwallo ko guda.

Duk da yake Najeriya tayi kokarin rama cin da kasar ta mexico tayi mata dab da tashin wasan, yanzu haka dai kasar Mexico ta sami nasarar lashe wasanni uku da kuma rasa guda a dukka wasannin shirye shiryen data buga domin tsare kanbinta a wasannin da za’a gudanar a kasar Brazil.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG