Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko "Aku" Zai Bada Sheda A Gaban Alkali!


Parrot
Parrot

Inda rai da lafiya, abun mamaki da al'ajabi baya karewa. Za’a gabatar da wani “Akkukuturu” da aka sani a turance “Parrot” a gaban alkali don ya bada sheda. Shi dai wannan Akun mai suna “Bud” an dauko shi daga kasashen Afrika ne, kuma yana zaune da mai gidan shi Mr. Martin Duram, mai shekaru arba’in da biyar 45, a karamar hukumar Ensley, a jihar Michigan, ta kasar Amurka.

Tun a shekarar da ta gabata ake gabatar da wata shari’a, tun bayan samun maigidan Akun Mr. Martin, kwance a cikin jini ya mutu, ana tuhumar waya kashe shi. A lokacin da ‘yan sanda suka isa gidan sun tarar da mutumin ya mutu haka itama matar mutumin Glenna, ta samu harbin bindiga a kanta.

Daga bisani an daura alhakin mutuwar Mr. Martin, a kan matar shi, da cewar ita ta kashe shi. Amma ‘yan ‘uwan mutumin sun bayyanar da cewar lallai matar ita ta kashe mijin nata, domin kuwa, sunji Akun yana bayanin yadda mutuwar mai gidan shi ta faru.

Don haka sun bukaci da a gabatar da Akun a gaban alkali, don tabbatar da cewar matar ita ta kashe mijin nata. Dalilin su kuwa shine, Akun yana fadan wasu kalmomi da suke bayyanar da abun da maigidan shi, ya fada kamin mutuwar ta shi. Sunce akun yana cewar “Kada ka harbe ni mutumin banza” Akun dai yanata mai-maita wannan kalmar, don haka yasa su kace ita ta kashe mijin nata. Yanzu haka dai ana jiran abun da ‘yan sanda zasu ce, dangane da gabatar da Aku a matsayin shaida gaban alkali.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG