Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zakuna "32" Sun Koma Gidan Gado, Bayan Shekaru Da Dama!


Lion
Lion

Alamu sun bayyanar da cewar, kasashen Afrika, na daya daga cikin kasashe da su kafi tausayin dabbobin dawa. A wani bincike da hukumar kasa-da-kasa masu kare hakkin dabbobi suka gudanar. Sun gano wasu zakuna 'yan asalin kasashen Afrika, da aka dauka daga yanki zuwa kasar Mexico shekaru da dama, ta kudancin kasar Amurka.

Wadannan zakuna a cikin tsawon shekaru da dama an azaftar da su, hakan ya bayyana ne a irin yanayin da aka same su ciki a kasar ta Mexico, na rashin abinci, isashiyar lafiya, ko kulawa ta musamman, alamu sun bayyanar da cewar an azaftar da su na tsawon lokaci.

Hakan yasa hukumar kare hakkokin dabbobi, daukar matakin da ba’a tabayi ba a duniya, na maida zakuna talatin da biyu 32, zuwa kasar Afrika ta kudu. Kwanaki kadan da maida zakunan kasar ta Afrika ta kudu, sai gasu sun fara walwala da nuna jin dadin yanayin da suka samu kansu. Hakan dai ya bayyanar da cewar kasashen Afrika, suna mutunta dabbobin daji fiye da ko ina a duniya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG