Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yanayin Zafi Na Kara Yawan Cuttuka A Duniya!


Kimanin shekaru billiyan 4.5 kenan da suka wuce, yanayin duniya yana canzawa sosai mautuka. Duniya kan fuskanci wasu canji masu kyau da ma’ana a wasu kuma lokkuta akan samu akasin hakan.

Ko a yau za’a iya ganin cewar abubuwa na canzawa a fadin duniya, wanda wasu daga ciki sukan faru ne haka nan, kamar yadda Allah yaso wasu kuwa sukan faru ne a sanadiyyar tallafi na dan’adam. Wadannan canje-canjen sukan faru ne a sanadiyar yadda yanayi ke canzawa, da yadda koguna ke kafewa ko gudana, haka da girgizar kasa, ambaliyan ruwa, da matsanancin zafi ko sanyi a fadin duniya. A jihar Alaska ta Amurka da akasanta da sanyi suma sun fara samun yanayin zafi wanda ya wuce kima, wanda kimanin shekaru 50 da suka wuce ba’asamun irin wannan zafin a yankin ba.

Masana na ganin cewar, duk hakan na faruwa ne a sanadiyyar yadda mutane ke bada tasu gudunmawa, kodai mutane na hawa abubuwan hawa da basu da isashiyar lafiya, ko kuma mutane basu zubar da shara yadda ya kamata, da ma yadda mutane ke gudanar da mu’amalar su ta yau da kullun. Akwai bukatar mutane su fara maida hankali wajen ganin sun taimaka wajen ganin an magance matsalar dumaman yanayi a duniya, a kuma kowane yanki suke. Akan samu cuttuka da dama a sanadiyar zafi, wanda hakan yake nufi mutane su samar da yanayi mai nagarta ga iyalan su a wannan lokacin na zafi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG