Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jerin Sunayen Mata Da Suke Tallafawa Tattalin Arzikin Duniya!


Operah Winfrey, tana daga cikin jerin mata masu kudi a duniya da suka samu kudin su batare da taimakon wani ba, itace ta takwas, tana da shekaru 62, wanda ta samu kudin ta a sanadiyar wasu shirye shirye da takeyi a gidan talabijin, tana da kimanin dallar Amurka billiyan $2.8B. Sai Wu Yajun, mai shekaru 51, tana sana’ar gidaje da filaye a kasar China, tana da adadin kudi da suka kai dallar Amurka billiyan $2.8B.

Ta tara kuwa a cikin jerin mata masu kudin a duniya, itace Giuliana Benetton, ‘yar kasar Italy, mai shekaru 78, tana sana’ar kayan sawa da kyale-kyale. Tana da kimanin dallar Amurka billiyan $2.7B. Sai ta goma kuwa itace Judy Faulkner, mai shekaru 72, 'yar kasar Amurka da take sana’ar kayan asibiti, tana da kimanin dallar Amurka billiyan $2.5B. Sai Zhang Xin, mai shekaru 50, da take sana’ar gidaje da filaye a kasar China itama, tana da kimanin dallar Amurka billiyan $2.5.

Itama Johnelle Hunt, ta zama ta goma a cikin jerin mata masu kudi a duniya inda take da shekaru 84, haka kuma tana da adadin dallar Amurka billiyan $2.5B, tana sana’ar sifiri, na motocin haya manya da kanana. Ta sha daya kuwa itace Marian Ilitch, mai shekaru 83, 'yar kasar Amurka, tana sana’oi da dama. Tana da fiye da dallar Amurka billiyan $2.4B.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG