Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Naira Miliyan 180, Kudin Sallamar Sunday Oliseh


Yanzu ya zama tilas hukumar kwallon kafa ta Najeriya, wato (NFF) ta tanaji Naira miliyan 180, idan har tana tunanin sallamar Sunday Oliseh, mai horas da ‘yan wasan Super Eagles.

An dade ana ce ce ku ce, akan ko Sunday Oliseh, zai ci gaba da kasancewa mai horas da ‘yan kungiyar ta Super Eagles, ko kuma a samo wani, bayan da suka sha kashi, a gasar cin kofin nahiyar Afirka, wanda aka gudanar a Rwanda.

Daga dukkan alamu, hukumar bata gaggawan sallamar Oliseh, saboda makudan kudaden da zata biyashi idan har tana bukatar ya bara matsayin san a mai horas da ‘yan wasan na Super Eagles.

Sunday Oliseh, dai ya sa hannu a kwantragin shekaru 3, ne kuma dududu yanzu watanin 7, kennan da kama ragamar horas da ‘yan wasan na Najeriya.

Koda yake Oliseh, yasan cewa ana son yin waje rod da shi amma yasan cewa za’a chake masa kudadensa.

XS
SM
MD
LG