Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mace Dauke Da Cikin Tagwaye Wata 6 Amma Bata Sani Ba!


A satin da ya gabata ne wata mata mai suna Shelby Mangani, a garin Ankeny a jihar Iowa, ta nan Amurka, ta wayi gari da ciwon mara, koda aka kaita asibiti, an dauki hoton cikin nata. Likitoci na dubawa sai suka ga tana dauke da juna biyu, kuma tagwaye ne.

Koda aka tambaye ta, tace ita bata da ciki kuma bata taba tsanmanin ace wai har tana dauke da tagwaye, domin kuwa bata taba jin wani alama ko wani abu da zai bayyana mata cewar tana da juna biyu ba. Koda aka duba sai aka ga cewar ai juna biyun ta, ya kai kimanin tsawon sati 34. Koda aka garzaya da ita dakin tiyata, an ciro tagwayen mata masu matukar kama da juna, likitocin sun bayyanar da cewar wadannan jaririran a lokacin da suke cikin mahaifa su, sun zauna a waje daya, shiyasa suke kamata da juna. Suka kara da cewar, mafi akasarin yaran da suka zauna a mahaifa daya basu cika rayuwa ba.

Tsakanin matar da mijin ta duk basu yadda da cewar wadannan ‘yayan su ne ba, domin kuwa basu tunanin haihuwa nan kusa. An dai sama yaran suna Ava da Anna, jim kadan bayan cirosu da akayi a cikin mahaifiyar su, kuma daya na da nauyin 4 pounds daya kuma nada na 3 pounds. Mahaifiyar yaran tace “Ina matukar son ‘yayan nan fiye da komai a duniya.”

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG