Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dokar Ta Bace Akan Dusar Kankara A Kasar Amurka


snow-2
snow-2

A jiya ne gwamna jihar New York, Mr. Andrew Cuomo, a nan kasar Amurka, ya bada wata sanarwar hana tafiye tafiye a cikin jihar. Sanadiyar yawan dusar kankara da aka samu tun daga ranar Juma'a zuwa yau, a yankin Arewa maso gabashin kasar. Sanarwar ta hada da mutanen da ke shiga cikin jihar daga makociyar jihar ta New Jersey, ta babbar gadar da ta hada jihohin biyu.

Haka ma a sanadiyar wannan dusar kankarar, duk ilahirin kamfanonin jiragen sama sun dakatar da tashi da saukan jirage a yankin. Hakan dai yasa dubun dubatan mutane suna tsaye a cikin tashoshin jirage, wanda ake tsanmanin kila sai zuwa yau da yamma ko gobe kamin a fara tafiye tafiye kamar koda yaushe.

Kimanin sama da mutane milliyan sittin ne ke fuskantar barazanar wannan dusar kankarar, da wata iska mai karfi, kana wannan dusar kankarar ta shafi jihohin Georgia har zuwa Massachusetts, haka kimanin mutane sama da 250,000 suke zaune a cikin gidajen su basu da wutar lantarki.

A jihohin Tennessee, Kentucky, North Carolina da Virginia kimanin mutane 9 ne suka mutu a sanadiyar haddura da aka samu na motoci a dai-dai lokacin da wannan dusar kankarar tazo. A jihar Virginia kadai akwai rahoto da kenuni da cewar, ansamu haddurran motoci sama da 1,000. Haka kuma wani mutun ya mutu a sakamakon bugun zuciya dai-dai lokacin da yake kokarin kwashe dusar kankara da ta taru a bakin gidan shi. Kimanin jihohi 11 suka saka dokar ta bace akan wannan dusar kankarar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG