Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abun Mamaki Jaririn "Panda" Yaki Yarda Da Dusar Kankara


Jaririn panda
Jaririn panda

Kimanin watannin shida ke nan da suka wuce, aka haifi wasu tagwayen dabobin da ake kira “Panda” wata dirkekiyar Panda mai suna “Mei Xang” bayan haihuwar tagwayen dayan ya mutu ya bara dayan. Shida dai jaririn pandan da matar shugaban kasar Amurka Michelle Obama da takwarar ta matar shugaban kasar China, Peng Liyuan, suka rada mishi suna “Bei Bei” sunan na nufin “Abun kauna da so” a watan Satunba.

Su dai dabbobin panda wasu irin hallita ne da Allah yayi su da suke rayuwa cikin dusar kakara, wanda basu iya rayuwa a inda yanayin su yake da zafi. Sukan rayu a kasashe da suke da sanyi da kuma dusar kankara.

Amma abun mamaki wannan Bei Bei panda daya kasance an haife shi a wani gidan zoo na Gundumar Kwalambiya a birnin Washington, ta nan kasar Amurka, ya saba da rainon mutane bana dabbobi a cikin daji ba. A shekaran jiya Alhamis aka samu saukar dusar kankara na farko a cikin wannan shekara, wanda ma’aikatan gidan zoo din, suka bashi damar ya fita wajen don yayi wasa da dusar kankara a karon farko a tarihin rayuwar shi. Sai suka ga bai aminta da yayi wasa da dusar kankarar ba domin kuwa bai saba da itaba.

A satin da ya wuce ne mutane sukayi ta tururuwa zuwa gidan zoo na Gundumar Kwalambiya don ganin wannan jaririn pandan a lokacin da aka fitar da shi don jama’a su ganshi. Dubban mutane sun taho daga garuruwa da dama na kusa da nesa, don suga wannan jaririn dabbar, gidajen jaridu da na talabijin da dama sun halarci wannan taron don ganin shi da bayyana ma al’umar kasar irin halin da yake cikiki bayan watanni shida da haihuwar shi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG