Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makarantar Da Ta Yaye Dalibai Manya Fiye Da Kowacce


Barewa College Zaria, na daya daga cikin makarantu da ta yaye manya-manyan dalibai da suka shugabanci kasar Najeriya, a baya, hakama har yanzu suna shugabanci a matakai daban-daban a kasar. Kama daga farar hula zuwa soja. Makarantar ta yaye dalibai manya da suka shugaban ci kasar fiye da kowace makaranta.

Tun bayan kafata da akayi a shekarar 1921, lokacin mulkin Gwamna janaral Hugh Clifford, na zamanin mulkin turawan mulkin mallaka, wanda a wancan lokacin ana kiranta “Katsina College” a birnin Katsina, sai daga baya aka maida ta “Kaduna College” a shekarar 1938, sai kuma “Government College Zaria” a shekarar 1949, kamin ta samun sunana “Barewa College”

Cikin wasu da makarantar ta yaye tun bayana kir-kirarta, sun hada da tsofafin shugabanin kasa, gwamnoni, ministoci, ambasadoji, da dai makamantan su. Ga wasu kadan daga cikin irin mutane da sukayi karatu a wannan makarantar.

1.) Alh. Ahmadu Bello, Premier of Northern Nigeria from 1954 to 1966

2.) Alh. Abubakar Tafawa-Balewa, Prime Minister of Nigeria from 1960 to 1961

3.) Gen. Murtala Mohammed, Military President from 1975 to 1976

4.) Gen. Yakubu Gowon(retd.), Military President from 1966 to 1975

5.) Alh. Shehu Shagari, President of Nigeria from 1979 to 1983

6.) Alh. Umaru Musa Yar'Adua, President of Nigeria from 2007 to 2010

7.) Mallam Adamu Ciroma , 3-time Minister (Industries; Agriculture; and Finance)

8.) Prof. Jubril Aminu - 2-time Minister (Education; Petroleum and Mineral Resources)

9.) Alh. Umaru Dikko - Minister of Transportation

11.) Alh. Ibrahim Mahmud Alfa, Ex-Governor of Kaduna State

12.) Mallam Nasir el-Rufai, Governor of Kaduna State

13.) Dr. Orji Uzor-Kalu, Ex-Governor of Abia State

14.) Alhaji Mohammed Bello - (current) Minister of FCT

15.) Lt. Gen. Abdulrahman Dambazzau(retd.) - (current) Minister of Interior

16.) Air Commodore Ibrahim Alkali(retd.) - Ex-Military Governor of Kwara State

17.) Prof. Bolaji Akinyemi - Ex-Minister of Education

18.) Hon. Justice Idris Legbo Kutigi - Former Chief Justice of Nigeria(CJN)

19.) Hon. Justice Uwais - Former Chief Justice of Nigeria

20.) Hon. Justice Mohammed Bello, Former Chief Justice of Nigeria

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG