Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekarar 2015 Na Iya Zama Shekarar Da Tafi Kowacce Zafi


Zafi
Zafi

Ana kallon shekarar 2015 da ke shirin karewa a matsayin shekarar da tafi kowace zafi a duniya. Rahoton majalisar dinkin duniya ta fitar da wannan rahoton. Mr. Michel Jarraud, shugaban hukumar binciken yanayi ta duniya, ya bayyanar da cewar ga dukkan alamu wannan shekarar na iya fin kowace shekar zafi, tun bayan fara kididdiga na yanayi a duniya.

A cewar hukumar tun cikin watanni 10, a cikin shekarar 2014 alkalunma suka fara nuna cewar shekara mai zuwa na iya yin zafi a wannan duniyar harma da cikin teku. Tun a tsakanin shekarun 1961 zuwa 1990 da aka samu alkalunman yanayi da suka kai “1.0 degree Celsius” ba’a sake samun hakan ba sai a wannan shekarar.

Majalisar dinkin duniya, bata cika fitar da rahoto ba, har sai shekarar ta kai karshe, amma a wannan karon saboda taron yanayi da za’a gudanar a kasar Paris, shiyasa suka fitar da wannan rahoton da zai bada kusan kwatan-kwacin abun da za’a iya samu a karshen shekara.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG