Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Apple Sun Kir-kiri Nasu Jirgin "iDrone"


us dron
us dron

Kamfanin Apple sunshiga tsere da abokanan hamanyansu wurin fitar da sabuwar na’ura mai tashi sama. Na’urar ana umfani da itane don daukar hoto, daukar bidiyo, da kuma sauraren sauti. Na’urar iDrone tanada kamarori guda hudu, da lasifiku guda hudu. Mutane zasu iya amfani da ita daga wayarsu ta iphone ko ipad ko Agogon Apple da kuma telebijin din Apple, don ta tashi sama ta kuma bi mutun a duk inda yake domin daukar hoto, daukar bidiyo ko sauraren wake-wake.

Wannan na’urar nadaga cikin hangen nesa da tsohon mai kamfanin Steave Job, yayi domin ganin Na’urorin kamfanin sun samu karbuwa, da kuma mahimmanci a wurin abokanna cinikin su. Sabuwar na’urar za’a iya sanar da ita abunda akeson tayi ta hanyar umfani da daya daga cikin wayar su ko agogonsu da sauran su. Sannan kuma mutun zai iya magana ga sifikunta domin bata umurnin abunda za tayi.

Kamfanin Apple sunyi bayani akan hangen nesa da sukema wannan na’urar na hanyar iya bata umurnin abunda zatayi, da kwakwalwar mutun. Suna tunanin cimma wannan burin ne ta sakama masu bukatar amfani da ita karamar na’ura a cikin kwakwalwarsu. Sannan zasu ci gaba da kula da aikinta da kara mata fa’idodi kowace shekara har zuwa shekaru goma sha biyar. Kamfanin dai suna kokarin fitar da wannan sabuwar na’urar ne tsakiyar sabuwar shekara.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG