Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Basira Da Hazaka Ba Yawan Shekaru Bane!


Zane
Zane

Grace Moon, tun tana ‘yar shekaru gomasha biyu 12, ta shiga wata gasa da kamfani “Google” na masu zane mafi kyau a duniya, a wancan lokacin shekarar 2008, taron masu zanen na sama da mutane dubu goma shashida16,000, ita tazo ta daya. Kowane yaro ko yarinya nada irin baiwar da Allah yayi musu, kodai na zane ko kokarin karatu.

Kamfanin na Google, suna da gasar yara matasa masu basirar zane, ‘yan makarantar sakandire, a wannan gasar tayi wani zane da kamfanin google suka sashi a shafin su. Kuma zanen ta yana daga cikin zane da akafi kallo a duniya a wannan lokacin. Ta samu kyautar kudi da suka kai dallar Amurka dubu goma $10,000 dai-dai da naira milliyan biyu da dubu dari uku 2,200,000 da kuma kudin makaranta da suka kai $25,000 dai-dai da naira milliyan biyar da dubu dari biyar 5,500,000 da kwamfutar hannu.

Shekaru bakwai kenan da suka wuce, sai gashi ta buga wani littafi na ire-iren zane da takeyi. Sabo da kyau da ma’ana na irin zane da take yi, yasa tazama wadda zanen ta ya zama wanda akafi kallo a duniya, domin kuwa an bayyanar da zanen ta a matsayin zane da mutane suka kalla a rana daya ,da yayi dai-dai da yawan mutane miliyoyi da suka shiga gidan tarihi, don ganin abubuwan tarihi. Manufa mutane sun nuna sha’awa matuka a irin zanen da take yi. Don haka yakamata matasa masu irin wadannan basirun su fara bayyanar da kanzu, ta fitar da irin zanene su kowa ya gani. A yanzu haka tana sayar da ire-iren zanen da tayi akan kudi masu yawa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG