Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

1 Cikin 3 Dake Mutuwa A Duniya! Nada Alaka Da Ciwon Zuciya


Zuciya
Zuciya

Cututtukan zuciya za su kasance da alhakin daya daga kõwanne mutun uku 3, da ke mutuwa a fadin duniya a wannan shekarun. Hakan na nuni da cewar anfi mutu a sanadiyar cutar zuciya. A yau da ban mamaki wannan hasashen na cewa ya kamata ace kowa daga kan matasa masu kanan shekaru, su maida hankali akan wasu abubuwa da zasu taimaka musu wajen gujema wadannan cututukan idan sun manyanta.

Ba lallai bane a kamu da wannan cutar ta hanya daya ba, amma hanya mafi kusanci da kamuwa da wannan cutar ta zuciya itace, yadda mutane ke cin abubuwa da suke kunshe da sinadarin “cholesterol” shi dai wannan sinadarin yana tarayya da jinin jikin mutun ne, wanda idan yayi yawa a cikin jinin mutun ya kana toshe wasu kafofi da jinni ba zai samu damar watayawa ba.

Makaman cikin jikin mutun basu iya samar da wannan cutar batare da abubuwa da mutane ke ciba, batare da la’akari da irin abun da ke kawo sinadari da zai iya cutar da rayuwar mutun. Shidai “cholesterol” a turance yana da matukar muhimanci ga rayuwar dan’adam, sai dai kuma idan yayi yawa yakan haifar da wasu matsaloli ga rayuwa mutun.

Don haka akwai buktar mutane su kiyaye cin wasu abubuwa, da kuma lura da adadin da suke ci, don guje ma cutar zuciya da sauran cuttutuka. Hanyoyi da suka kamata mutane subi don gujema wannan cuttutukan, sun hada da motsa jiki, cin ‘yayan itatuwa, cin abinci mai gina jiki, rage yawan tunani, rage yawan ayyukan karfi, cin abinci da adadi, da dai abubuwa makamantan haka. Idan mutun ya fuskanci wasu abubuwa na daban a jikin shi to ya garzaya asibiti don ganin likita.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG