Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mu'amalar Yau Da Kullun Na Bayyanar Da Tsufan Mutun


Skin Lightening Creams
Skin Lightening Creams

Tsufa wani abu ne da baza’a iya guje ma ba, amma duk da haka mutun kan iya zama mai kananan shekaru idan ansan wasu sirrin gyaran jiki. Idan har mutun na yawaita jin kasala a rana, kuma ya kanga wasu zane a fuskar shi da safe, to mutun yasani cewar yadda yake gudanar da rayuwar shi na bada gudun mawa wajen tsufan mutun.

A cewar wasu masana, mutun zai iya maida hannun agogo baya, yin wasu dubaru da zasu taimaka mishi wajen zama matasahi ko bayan shekarun shi su ja. Suka ce akwai bukatar matasa tun da kuruciyar su kada su yawaita yin bacci da dare, domin suna ganin idan mutun yana yawan bacci wannan zai kara taimakawa wajen fatar shi ta jeme. Haka kuma idan mutun ya yawaita kwantawa bacci cikin baccin rai, to hakan nasa fatar kusan idon shi ta zagwanye, wanda zai saurin nuna tsufan shi, kuma ga masu shan maganin bacci shima yana da hatsari ga lafiyar jikin mutun.

Hakama yadda mutun ke gudanar da rayuwar shi, a yau da kullun yakan kara taimakawa wajen tsufan mutun. Abun nufi a nan shine kada mutun ya cika yawan fada, ko hayaniya, da yawan magana, duk wadannan dabi’un sukan tai maka wajen tsufa da wuri. Kana shiga cikin wajajen da basu da iska mai kyau shima yana kara taimakawa wajen fata ta nuna tsafa da wuri. Don haka akwai bukatar matasa, su yawaita motsa jiki cin abubuwa masu gina jiki da yin wanka akai-akai, shafa mai masu sinadaran gina fata, duk sune abubuwa da zasu taiamaka wajen komawa matasa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG