Wani karamin jirgin sama mai ingin daya, ya yi wata sauka a kan babban titin motoci, a kan babbar hanyar mota mai lamba 84, a jihar Idaho, ta nan kasar Amurka. Wannan titin na daya daga cikin tituna masu hada-hada sosai, a dai-dai lokacin da jirigin ya sauka, yayi dai-dai da lokacin zirga-zirga mutane sosai wajen kokarin zuwa wajen aiki.
Jami'ai biyu na hukumar 'yan kwan-kwan sun ce, jirigin ya sauka ne da kamar karfe bakwai 7:00am na safe. Rahotannin da suka fito jim kadan bayan abkuwar abun, na nuni da cewar babu wani rauni ko kuma wani hadari da ya shafi motoci.
Babu dai wani bayani da ke nuni dacewar, ko jirgin ya samu tangardar ingin ne, wanda yasa ba zai iya isa zangon shi ba, amma a lokacin da jirigin ya sauka, daya daga cikin farfelar jirigin ta lankwashe. Duk da haka jirkin na da sauran kimanin awa daya kamin ya kai masaukin shi na karshe, sai ga abkuwar abun.